3 Nuwamba 2025 - 16:32
Source: ABNA24
Kwamandan CENTCOM Ya Gana Da Firayim Ministan Da Ministan Tsaron Qatar

Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka (CENTCOM) ya yi tafiya zuwa Qatar inda ya gana da kuma yin tattaunawa daban-daban da Firayim Ministan kasar da Ministan Tsaro.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: A cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar, taron ya tattauna dangantakar dabaru mai zurfi tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin tallafawa da karfafa su, musamman a fannin hadin gwiwa tsakanin sojoji da tsaro. Bangarorin biyu sun kuma tattauna batutuwa da dama masu muhimmanci.

Abin la’akari ne cewa: Jami'in Amurkan ya taba ganawa da kuma tattaunawa da Saud bin Abdulrahman Al Thani, Ministan Tsaro da Mataimakin Firayim Ministan Qatar.

Kwamandan CENTCOM Ya Gana Da Firayim Ministan Da Ministan Tsaron Qatar

Your Comment

You are replying to: .
captcha